ABNA24 : Jami’an Diflomasiya sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, an kai hare-haren makaman roka a birnin Asmara na Eritrea a karshen mako, inda makaman suka dira a kusa da filin jiragen saman birnin.
Dakarun Habasha dai na amfani da wannan filin jirgin saman kamar yadda tsagerun Tigary suka bayyana cewa, inda suke ganin ya halatta su kai wa filin jirgin farmaki.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce, ya bada umarnin kaddamar da aikin soji a yankin na Tigray a daidai lokacin da tankiyarsa da jam’iyyar tsagerun da ke mulkin yankin ta tsananta.
Jam’iyyar ta TPLF ta zargi gwamnatin Abiy da samun tallafin soji daga Eritrea, ikirrain da gwamnatin ta musanta.
Yanzu haka dai, wannan rikici ya tilasta wa Habashawa sama da dubu 25 tserewa daga muhallansu domin neman mafaka a kasar Sudan , adadin da zai ci gaba da karuwa a cewar hukumomin Sudan.
342/